Sayyid Abdul Malik AlHouthi yayin mayar da martani ga kafa kawancen yaki akan Yemen: Kada ku sadaukar da kanku wajen yi wa Isra’ila hidima.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Sayyid Abdul Malik AlHouthi yayin mayar da martani ga kafa kawancen yaki akan Yemen: Isra’ila na neman shigar da wasu ƙasashen a cikin yakin tallafawa jiragen ruwanta, amma abin da Amurka da Isra’ila suka yi bai hana mu ayyukanmu na ka’ida ba.
Ayyukanmu ba su nufi jigilar kaya da jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa ba, kawai sun shafar jiragen ruwa da ke da alaƙa da sahyoniyawa ne.
A wani labarin na daban an gudanar da bikin kaddamar da sabbin wallafe-wallafen Majalisar Ahlul-baiti (AS) tare da halartar Ayatullah Ramazani, babban sakataren wannan majalissar.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da taron bukin kaddamar da sabbin wallafe-wallafe na Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ta duniya kafin sallar azahar a yau Alhamis 30 ga Azar 1402 wanda yayi daidai da 21 ga watan Disamba 2023 tare da jawabin Ayatullah Ramazani babban sakataren wannan majalisar da kuma Ayatullah “Dari Najaf Abadi” mataimakin shugaban majalisar koli ta majalisar a ginin majalisar Ahlul-Baiti (AS) da ke birnin Qum.
An Fassarar Littafai 110 A Majalisar Ahlul Baiti (AS) Zuwa Harsuna 22 Na Duniya.
Hujjatul-Islam Walmuslimeen Mehdi Farmanian mataimakin shugaban majalisar duniya ta Ahlul Baiti (As) a fannin kimiya da al’adu na Ahlulbaiti (a.s) a cikin wannan biki, yayin da yake ishara da ayyukan wannan majalissar a fagen fassarar littafai, ya bayyana cewa: Daga cikin Ayyukan Mataimakin Shugaban Kimiyya da Al’adu na Majalisar, shine fassarar mujalladan littattafai 110 zuwa harsuna 22. Wanda Za a bayyana tare da gabatar da waɗannan ayyukan a yau. Manufarmu ita ce, a buga littattafan a cikin ƙasashen da aka yi niyya kuma a shirye muke mu ba da haɗin kai don buga waɗannan littattafai a ƙasashen waje.
Ya ci gaba da cewa: Daga cikin littafan da aka tarjama majalissar Ahlul-baiti (AS) a bana, littafai 18 cikin harshen Turkanci, littafai 11 a Yaren Hausa, littafai 9 cikin harshen faransanci, littafai 9 a cikin yaren Turanci, litattafai 7 a yaren Pashto, litattafai 6 a cikin yaren Indonisiya, littafai 6 cikin harshen Larabci, littafai 5 cikin harshen Swahili, littafai 5 cikin harshen Urdu, littafai 4 cikin harshen Urdu da kuma 4 a Yaren Tajik.
Mataimakin shugaban majalissar Ahlul Baiti (AS) a fannin kimiya da al’adu ya kara da cewa: “Wiki Shi’a” mai suna “Wiki Shi’a” na daga cikin abubuwan karramawa na majalissar ilimi da al’adu ta majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, wadanda adadinsu ya kai Harsuna 22 kuma suna samun masu ziyaratarsu miliyan 14 a kowane wata.
A wannan shekara, an ƙara mashiga 6,000 zuwa Wiki ta Shi’a, kuma adadin waɗannan mashigar zai kai 8,000 a ƙarshen shekara, kuma yanzu akwai mashigar kafa 32,000 a cikin harsuna 22 a cikin Wikin Shi’a.
Source: ABNAHAUSA