Amman (IQNA) Wata shahararriyar kungiya a kasar Jordan ta yi kira da a hana fitar da kayayyakin noma daga wannan kasa zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Arabi 21 cewa, majalisar ba da goyon bayan gwagwarmaya da tsaron kasar ta Jordan ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar aikin gona da nufin hana fitar da kayan lambu ga gwamnatin mamaya na Isra’ila saboda laifukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta aikata a zirin Gaza .
Wannan majalisa ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa za a gudanar da wannan bikin a gaban ma’aikatar noma a yau Litinin.
A halin da ake ciki kuma akwai rahotannin da ke cewa akwai hanyar da za a bi wajen fitar da kayan lambu daga kasar Jordan zuwa yankunan da aka mamaye.
Sanarwar ta ce: “An killace Gaza da yunwa yayin da ake fitar da kayan lambu daga kasarmu zuwa Isra’ila. Dakatar da fitar da kayan lambu zuwa ga gwamnatin sahyoniya.
Kasar Jordan ta musanta cewa akwai wata hanya ta kasa tsakanin Dubai da Saudiyya da ta ratsa ta kasar Jordan, kuma ake amfani da ita wajen jigilar kayayyaki zuwa ga gwamnatin mamaya.
Kamfanin dillancin labaran kasar Jordan Petra ya nakalto majiyar ma’aikatun sufuri da masana’antu da kasuwanci na cewa: Labarin da ake dangantawa da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta na Isra’ila cewa akwai wata gadar kasa ta tashar jiragen ruwa ta Dubai da ta ratsa daga Saudiyya da Jordan domin jigilar kayayyaki. ga Isra’ila, ba gaskiya ba ne ko kaɗan.
A cikin wata sanarwa da ta aikewa kamfanin dillancin labaran, majiyar ta kara da cewa: Matsayin gwamnatin kasar Jordan dangane da goyon bayan Falasdinawa da kuma tsayawa tare da su ta kowace hanya a fili yake.
Majiyoyin jami’an kasar Jordan sun ce an musanta irin wadannan ikirari, kuma wadannan labarai na da nufin kawo cikas ga tsayuwar daka a kasar Jordan dangane da mumunar zaluncin da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a yakin Gaza.
Majiyoyin yada labaran Isra’ila da suka hada da gidan yanar gizo na Hebrew Walla a baya sun bayar da rahoton aikin wata gadar kasa daga tashar jiragen ruwa ta Dubai a madadin jiragen ruwa da ke ratsa tekun Bahar Maliya ta Saudiyya da Jordan don shigo da kayayyakin abinci zuwa Isra’ila.
Source: IQNAHAUSA