Hadin Gwiwar Tarayyar Turai Da Gwamnatocin Yammacin Turai 14 Sun Yi Allawadai Da Laifukan Ta’addaanci Na Mazauna Yammacin Kogin Jordan
Sanarwar hadin gwiwa ta Tarayyar Turai da gwamnatocin Yammacin Turai 14 / Wajen Yin Tir Da Laifukan Mazauna Yammacin Kogin Jordan
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya kawo maku rahoton wata sanarwar da hukumokin kashashen Turai bisa na kaltowa daga kamfanin labarai na IRNA cewa Kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Turai 12 tare da Canada da Ostireliya sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah wadai da hare-haren na dabbanci da matsugunan yahudawan sahyuniya suka kai a yammacin gabar kogin Jordan a cikin kakkausar harshe tare da jaddada cewa irin wadannan ci gaban ta’addaci na barazana ga samun dauwamammen zaman lafiya a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA a ranar Juma’a ya fitar da cewa, a cikin wannan sanarwa da aka buga kwafinta a shafin yanar gizon gwamnatin Birtaniya, an bayyana cewa, kasashen Australia, Belgium, Denmark, Tarayyar Turai, Finland, Faransa, Ireland, Luxembourg, Netherlands, Norway ,Spain,Sweden,Switzerland,Britaniya da Canada na son gwamnatin Isra’ila ta dauki matakan gaggawa don tunkarar tashe-tashen hankula da ba a taba ganin irinsa ba na mazauna yankin yammacin kogin Jordan.
Sanarwar ta ce, muna yin Allah wadai da ta’addancin masu tsattsauran ra’ayi da ke addabar al’ummar Palastinu. Muna kara jaddada matsayinmu cewa matsugunan gwamnatin sahyoniyawan da suke mamaya a gabar yammacin kogin Jordan haramun ne bisa dokokin kasa da kasa, muna tunatar da wannan gwamnati wajibcin da ya rataya a wuyanta kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, musamman a shafi na 49 na yarjejeniyar Geneva ta hudu.
Marubutan wannan bayani sun jaddada cewa: ba za a amince da karuwar tashin hankalin masu tsattsauran ra’ayi kan Falasdinawa ba. A matsayinta na mamaya, dole ne Isra’ila ta kare fararen hular Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan, sannan kuma a gurfanar da wadanda ke da hannu a rikicin.
Bangarorin Yamma sun yi gargadin cewa: gazawar Isra’ila wajen tallafa wa Falasdinawa da hukunta masu tsattsauran ra’ayi, ya sa tashin hankalin mazauna yankin ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, kuma ci gaba da hakan zai raunana tsaron yammacin kogin Jordan da kuma yankin da kuma yin barazana ga makomar yankin na zaman lafiya mai dorewa.
A cikin wannan bayani, an bukaci gwamnatin sahyoniyawan da ta dauki kwararan matakai don tabbatar da samun goyon baya mai inganci da gaggawa ga al’ummar Palasdinu.
Kalmomi da aka furta suna da mahimmanci, a cewar mawallafin bayanin, “amma yanzu dole ne a aikata su a aikace.”
A cewar wannan sanarwa yahudawan sahyuniya sun kai hare-hare fiye da 343 a yammacin gabar kogin Jordan tun daga watan Oktoban bara, inda aka kashe fararen hula Falasdinawa 8, sama da mutane 83 suka jikkata, yayin da wasu 1026 suka tilastawa barin gidajensu.
Kamfanin dillancin labaran Irna: yayin da kasashen duniya suka mayar da hankali kan matsalar jin kai a zirin Gaza, ci gaba da tashe-tashen hankula da kisan gilla da ake yi wa Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan ya kara haifar da damuwa a kasashen yammacin duniya dangane da fadada yakin da kuma kara ruruwa rikice-rikice.
Makwanni biyu da suka gabata ne Amurka ta haramta ba wa sahayoniya da masu tsattsauran ra’ayi takardar biza shiga kasarta.
A baya sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya sanar da cewa, a karkashin sabuwar siyasar manufar Amurka, “wadanda da suka taka rawa wajen kawo cikas ga zaman lafiya, tsaro ko zaman lafiya a yankin yammacin kogin Jordan, ciki har da tada tarzoma ko kuma daukar wasu matakai kan fararen hula za’a su ake nufi da wannan hukunci.
Ba tare da yin tsokaci kan kisan da aka yi wa Falasdinawa sama da 18,000 a zirin Gaza ba, Blinken ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da shugabannin gwamnatin Isra’ila don nuna cewa dole ne gwamnatin ta kara yin kokarin kare fararen hula Falasdinawa daga hare-haren masu tsattsauran ra’ayi.
Ita ma kungiyar tarayyar turai tana shirin kakaba irin wannan takunkumin a kan sahyoniyawa masu tsattsauran ra’ayi. Josep Borrell, mai kula da manufofin ketare na kungiyar EU a ranar Litinin din da ta gabata, a karshen taron majalisar ministocin, ya ce za a sanar da matsayin hukuma da shirin sanya takunkumi na wannan kungiyar cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ministan harkokin wajen Birtaniya David Cameron ya sanar a jiya cewa, an haramta shiga kasar ga tsageran sahyoniyawan da suke zaune a kasar.
Da yake bayyana cewa “dole ne Isra’ila ta dauki tsauraran matakai don dakatar da tashin hankalin mazauna yankin da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin”, ya yi gargadin cewa: “Muna hana mazauna da ke da alhakin tashe-tashen hankula a gabar yammacin kogin Jordan shiga Burtaniya don tabbatar da cewa babu irin wadannan mutanen masu aikata wadannan munanan ayyuka agidajenmu.
Source: ABNAHAUSA