Kamfanin jiragen ruwa na Ambury na Birtaniya ya sanar da kai hari ta sama kan wani jirgin ruwan Laberiya a tekun Bahar Maliya.
An kai hari kan wani jirgin ruwa na kasuwanci a mashigar Bab Al-Mandeb
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya nakalto maku daga kamfanin labarai na IRNA cewa kamfanin jiragen ruwa na Ambury na kasar Britaniya ya sanar a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a cewa an kai hari kan wani jirgin ruwan kasuwanci mai dauke da tutar kasar Laberiya a lokacin da yake wucewa ta mashigin Bab al-Mandab. An ce wasu sassan jirgin sun kone kurmus inda daya daga cikin kwantenan ta fada cikin teku.
A cewar Ambri, an kai wa wannan jirgin ruwan na kamfanin Hapag hari ne a lokacin da yake wucewa ta mashigir Bab al-Mandeb da ke kudancin tekun Bahar Maliya kusa da tashar ruwan Mokha a kasar Yemen.
Kamfanin na Burtaniya ya bayyana cewa sojojin Yemen ne suka kai harin kan jirgin. Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin wannan harin.
Hukumar kula da harkokin kasuwanci ta ruwa ta Birtaniya UKMTO ta kuma sanar da cewa, ta samu sakon gargadi daga wani karamin jirgin ruwa na kasar Yemen da ke ba wa jirgin umarnin sauya hanyarsa zuwa kasar Yemen.
Bisa wannan rahoto, kungiyar gwagwarmayar kasar Yemen ta sanar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila.
Source: ABNAHAUSA