Bankin Duniya ya sanar da ba da tallafin dala miliyan 20 a Gaza
Bankin Duniya ya sanar da ba da sabon tallafin dala miliyan 20 don samar da taimakon jinƙai ga al’ummar Gaza, da ya haɗa da dala miliyan 10 don sayen kayan abinci.
Sanarwar da bankin ya fitar ta ce, tallafin zai kai ga kimanin mutum 377,000, wani ɓangare ne na wani babban shirin agaji na dalar Amurka miliyan 35 ga Zirin Gaza.
Sanarwar ta ce an riga an kai dala miliyan 15 na farko na agajin gaggawa.
1226 GMT — Falasdinawa da ake tsare da su a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye sun kai 3,810
Sojojin Isra’ila sun sake kama wasu Falasdinawa 51 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, inda adadin waɗanda suka kama zuwa yanzu ya kai 3,810 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta.
A cikin wata sanarwa da kungiyar fursunonin Falasdinu ta fitar ta ce yawancin fursunonin an tsare su ne a birnin Jenin.
A gefe guda kuma sojojin na Isra’ila sun kai farmaki kan garin Silwad da ke gabashin birnin Ramallah tare da yi wa mazauna yankin tambayoyi da dama kafin su sako su, kamar yadda wakilin Anadolu dake wajen ya bayyana.
0132 GMT — MDD ta yi wa Gaza lakabi da ‘Jahannama a duniya’ yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare
Sojojin Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai a wurare da dama a Zirin Gaza da ake ragargaza a daidai lokacin za a kada kuri’a a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan wata sabuwar bukatar tsagaita bude wuta.
Sama da wata biyu da fara yaƙin ranar 7 ga Oktoba, babban jami’in hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD Philippe Lazzarini, ya kwatanta Gaza da “Jahannama a doron ƙasa”.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na fargabar yunwa da cututtuka za su mamaye yankin na Falasdinu nan ba da jimawa ba, suna roƙon Isra’ila da ta ƙara ƙaimi wajen kare fararen hula.
1218 GMT — Karacin iskar oxygen ya yi sanadin mutuwar yara uku a asibitin Gaza
Yara uku sun rasu a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza sakamakon karancin iskar oxygen.
Daraktan asibitin ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Sojojin na Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a asibitocin Gaza, inda ko a yau Laraba sai da rahotanni suka ce sojojin sun afka asibitin na Kamal Adwan.
Yara ne suka fi yawa a cikin dubban mutanen da Isra’ila ke ci gaba da kashewa a Gaza.
1113 GMT — Mayakan Houthi sun dauki alhakin kai hari kan jirgin ruwan da zai je Isra’ila
‘Yan tawayen Houthi a ranar Talata sun sanar da cewa sun kai hari kan wani jirgin ruwan kasar Norway dauke da man fetur wanda ke hanyar zuwa Isra’ila.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Yahya Saree ya fitar, ya bayyana cewa sun kai wa jirgin ruwan hari ne a Bahar Maliya bayan jirgin ya ki jin gargadin da suka yi.
Tun a kwanakin baya mayakan na Houthi suka yi gargadi ga jiragen ruwa masu zuwa Isra’ila.
Yahya ya bayyana cewa akwai jiragen ruwa da dama a kwanakin biyun da suka gabata wadanda suka ji gargadinsu, sai dai a cewarsu, jirgin na kasar Norway ya yi kunnen kashi.
Source: TRTHausa