Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya kamata Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sauya tsattsauran ra’ayin gwamnatinsa inda ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra’ila ta hana tabbatar da kasar Falasdinu ba, sai dai Netanyahu ya yi raddi cewa Amurka ta jefa “bama-bamai masu guba” a Japan.
Biden ya yi tsokacin ne a wurin bikin tara masa kudi na yakin neman zabensa na 2024 bayan Amurka ta sayar wa Isra’ila tankokin yaki 14,000 ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba sannan ta hau kujerar-na-ki lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya nemi amincewarta game da kudurin da ke neman Isra’ila ta tsagaita wuta a Gaza.
Biden ya shirga karya cewa “galibin kasashen duniya suna goyon bayan” Isra’ila, duk kuwa da zanga-zangar da ake ta gudanarwa a fadin duniya na kyamarta tun daga 7 ga watan Oktoba sannan kasashe mambobin Kwamintin Tsaro na MDD da ma mambobin Babban Zauren MDD sun yi tarayya wajen kira a kawo karshen cin zalin da Isra’ila take yi wa al’ummar Gaza.
“Amma yanzu su (Isra’ila) sun soma rasa goyon baya saboda yadda suke kai hare-haren bama-bamai irin na kan mai-uwa-da-wabi,” in ji Biden.
Biden ya yi wadannan kalamai ne a yayin da mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro, Jake Sullivan, yake shirin tafiya Isra’ila domin tattaunawa da majalisar da ke aiwatar da yaki ta kasar.
Biden ya ambaci dan siyasar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir, wanda shi ne ministan tsaron kasa na Isra’ila, inda ya ce “wannan ce gwamnati mafi tsattsauran ra’ayi a tarihin Isra’ila.”
“Ya kamata [Netanyahu] ya canza gwamnatinsa. Wannan gwamnatin ta Isra’ila tana sanya abubuwa suna yin tsauri,” a cewar Biden. Ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra’ila “ta ki yarda” a kafa kasar Faladinu ba, matakin da masu tsattsauran ra’ayi na Isra’ila suke adawa da shi.
Biden ya yi tsokaci a game da wata kebantacciyar hira inda firaministan Isra’ila ya ce: “‘Ku [Amurkawa] kun jefa bama-bamai a Jamus, kun jefa bama-bamai masu guba da suka kashe dimbin kananan yara.'”
Biden ya ce ya mayar da martani da cewa: “Eh, haka ne shi ya sa bayan Yakin Duniya na Biyu aka samar da tsare domin ganin irin wannan bai sake faruwa ba… kada ka maimaita kuskuren da muka lokacin harin 9/11. Babu wani dalili da ya sa muka yi yaki a Afghanistan.”
Source: TRTHausa