Hukumar dake kula da gasar firimiya ta Ingila tana tuhumar kungiyar Manchester City da laifin kasa tsawatarwa ‘yan wasanta a wasan da suka tashi 3-3 da Tottenham a gasar Premier League.
‘Yan wasan Manchester City sun gewaye alkalin wasa, Simon Hooper, wanda ya bayar da bugun tazara dab da za a tashi a lokacin da kwallo ta je wajen Jack Grealish bayan da ya nufi raga.
Tun farko Hooper bai busa ketar da aka yi wa Erling Haaland ba, amma kwallo na zuwa wajen dan wasan tawagar Ingila sai kawai ya busa usur domin a dawo a buga ketar da aka yi tun farko.
Haaland yana daga cikin ‘yan wasan Manchester City da suka fi korafi a fafatawar, har ma ya caccaki alkalin wasan a dandalin sada zumunta na D, wanda hakan watakila shi ma ya sa a tuhume shi.
Wasa na uku kenan da tawagar ta Guardiola ta yi canjaras a Premier League a jere, bayan 4-4 da Chelsea, da kuma 1-1 da Liberpool kuma hakan ne ya sa Manchester City ta koma ta ukun teburin babbar gasar kwallo ta Ingila da maki 30, da kuma tazarar maki daya tsakaninta da Liberpool.
A wani labarin na daban dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Alex Iwobi ya jefa kwallaye biyu a wasan da kungiyarsa ta Fulhma ta lallasa abokiyar karawarta Nottingham Forest da ci 5-0.
Iwobi ya fara jefa kwallo a minti na 30 da fara wasan kafin ya jefa ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Nasarar da Fulham ta samu akan Forest yasa ta koma matsayi na 12 akan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Iwobi ya koma Fulham daga kungiyar kwallon kafa ta Everton a bana, inda zuwa yanzu ya jefa kwallaye 4 a wasanni 13 da ya buga mata.
Source: LEADERSHIPHAUSA