Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙungiyar masu saka tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai da sada zumunta su mayar da hankali wajen faɗakar da ‘yan Nijeriya kan sababbin tsare-tsaren tattalin arziki waɗanda gwamnatin Tinubu ta zo da su, waɗanda burinsu shi ne haifar da cigaban ƙasa ta fuskar tattalin arziki.
Idris ya yi kiran ne a ranar Alhamis a Abuja a lokacin buɗe babban Taron Masu Tallace-tallace na Ƙasa mai taken “Sadarwar Talla a Matsayin Mai Kawo Nagartaccen Sauyi Ga Ƙasa”.
A cewar hadimin musamman na ministan kan yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim a wata sanarwa da ya fitar, inda yace, ministan ya samu wakilcin Darakta-Janar na Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu, ya yi la’akari da muhimmiyar rawar da ƙwararrun masu sana’ar tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen yaɗa labaran da za su yi tasiri a wajen jama’a.
Ya ce su na kan cikakken matsayin da za su iya jan akalar samun sauyi a tsarin tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya ta hanyar yi wa jama’a yekuwar yadda za su ci moriyar sababbin tsare-tsaren da gwamnatin ke aiwatarwa.
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ƙananan sana’o’i, da Shirin Shugaban Ƙasa na Bada Rance Bisa Ƙa’idoji da shirye-shiryen rage raɗaɗin rayuwa, waɗanda aka yi domin ‘yan kasuwa, masu aikatau, masu sufuri, ‘yan talla, da masu ayyukan fasaha da bada ƙananan rance.
“Sana’o’i mafi ƙanƙanta a ƙasar nan su miliyan 1 za su ci moriyar rancen kuɗi N50,000 kowannen su, yayin da manyan sana’o’i za su ci moriyar rance daga Asusun Naira Biliyan 75 da aka tanadar.”
Ministan ya ƙara da cewa waɗannan shirye-shiryen ɗori ne a kan waɗanda da ma can an bayyana su kuma ana aiwatar da su, misali samar da motocin safa-safa masu aiki da hasken rana da gwamnatocin jihohi za su ƙaddamar, domin rage wahalar da cire tallafin man fetur ya janyo.
Ya ce duk waɗannan tsare-tsaren ba wai an yi su da ka ba ne, a’a, sai da aka tsara su a tsanake cikin Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaban Ƙasa, wadda ta haɗa da sauya fasalin tattalin arziki don a samar da cigaba mai ɗorewa; ƙarfafa tsarin tsaro don samar da kwanciyar hankali da arziki; haɓaka aikin gona don wadata ƙasa da abinci; buɗe hanyoyin makamashi da ma’adinai don samun cigaba mai ɗorewa da kuma bunƙasa hanyoyi da gine-gine a matsayin su na turakun kawo cigaba.
Sauran su ne: bada muhimmanci ga harkokin ilimi, kiwon lafiya, da taimakon jama’a a matsayin muhimman ginshiƙan cigaban ƙasa da gaggauta faɗaɗar hanyoyin tattalin arziki ta hanyar masana’antu, aiki da komfuta, fasahohin zamani, ƙere-ƙere, da ƙirƙire-ƙirƙire.
Ministan ya ce wannan gwamnatin ta sadaukar da kan ta ne ga samar da bayanai a kan lokaci kuma ta nagartacciyar hanya, kuma ya bada tabbacin cewa zai gudanar da aikin da aka ɗora masa a buɗe kuma a mutunce.
Ya ce: “A yayin da mu ke bada bayani ba tare da ɓoye komai ba kuma a cikin nagarta, ina kira a gare ku a matsayin ku na ƙwararru da ku tattaro ƙwan ku da kwarkwatar ku ku taimaka mana domin mu isar da bayani dalla-dalla ga jama’a ba tare da wata hargowa ko sauya shi ba.”
Source: LEADERSHIPHAUSA