Shugaban kwamitin amintattu na Abuja Literacy Society, Ferdinad Agu, ya ce, cigaba da amfani da hanyoyin fasaha za su kai ga ingantawa da bunkasa harkokin gudanar da zabe a Nijeriya.
Ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta kara dagewa wajen amfani da fasahar zamani a dukkanin ayyukanta domin kyautata harkokin zabe.
Agu, kwararren mai zane ne, ya shaida hakan ne a lokacin da ke gabatar da makala mai taken amfanin fasaha a bangaren shugabanci, a wajen taron gabatarwa da mika lambobin yabo ta Professional Leadership Practitioners Institute (PLPI) da ya gudana a (LCCI), Alausa, Ikeja.
Agu ya kuma jaddada muhimmancin amfani da fasaha da cewa na taimakawa matuka wajen cimma nasarori. A cewarsa, mutane sun kara yarda da INEC a lokacin da ta yi alkawarin cewa za ta yi amfani da fasaha a yayin zaben 2023.
Ya kuma shawarci INEC da ta rungumi tsarin nan na hulda da kudade ta yanar gizo ba kash ba, inda ya ce, hakan zai rage wasu abubuwan da ke tafiya ba daidai ba.
Agu ya ce: “Da INEC za ta yi irin abun da cibiyoyin kudi suka yi, duk da ‘yan matsalolin da tsarin karancin kash din kudi a hannun mutane, idan har da INEC za ta dage, tabbas da za a samu tagomashi matuka. Zai kuma iya yiyuwa.” “Kada mu zauna mu ce Nijeriya ba za ta cigaba ba, Nijeriya ba za ta inganta ba. Ba mu da wani zabin da ya wuce mu amince kan cewa fasaha da jagoranci na tafiya ne kafada da kafada.”
Ya ce, matsalolin da ke akwai shi ne a bangaren shugabannincin ba a rungumar fasaha yadda ya dace a bangarorin gudanar da harkokin gwamnati.
Agu “Akwai bukatar mu sake tunani. Domin cimma nasarar fasaha a bangaren jagoranci da cigaban kasa, muna da bukatar yin tunanin hanyoyin ayyuka, inganta rayukan al’umma, musamman wadanda aka yi watsi da su.
Dole ne mu kirkiri damarmaki ta hanyar amfani da fasaha.”
Source: LEADERSHIPHAUSA