Biyo bayan harin bom da jirgin sojin Nijeriya ya jefa a kan masu gudanar da bikin Maulidi a Kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, MALAM MUSA ABUBUKAR.
Wakilinmu SHEHU YAHAYA ya ziyarci kauyen tare da samun nasarar tattaunawa da dattijo mai shekara 74 da haihuwa, MALAM MUSA ABUBAKAR wanda ya tsallake rijiya da baya, inda ya bayyana irin abubuwan da ya gani yayin harin na bom. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:
Baba ko za ka bayyana mana sunanka da kuma matsayinka a wannan gari?
Sunana Malam Musa Abubakar, sannan ni dattijo ne mai shekara 74 da hauhawa, a wannan kauye na Tudun Biri aka haifi iyayenmu, haka nan mu ma a nan aka haife mu.
Ko wannan gari yana da tarihin ta’addanci ne?
Ko daya ba ma harka da ‘yan ta’adda, har ila yau kuma ba ma koyi da su, domin kuwa ba halinmu ba ne a nan Tudun Biri.
Ko za ka iya fada mana abin da ya faru a wannan gari?
A gabana abin ya faru a daidai wurin nan (yana mai nuna kusa inda yake zaune), kujerata tana kusa da wurin da ake taron Maulidin ina zaune, saboda ni ne mutum na farko da ya fara zuwa wurin wannan taro. Sannan, yaran da aka kashe ina zaune suka zo, can sai na ji wani abu ya yi sama ya yi kara, sai aka zo aka ce min, Baba ba ka ji rauni ba? Sai na ce a’a babu abin da ya same ni, domin babu rauni a jikina; haka na tashi na kakkabe babbar rigata na mike, sai dan wannan jinin da kuke gani a jikin rigar tawa shi kadai ne abin da na san ya faru da ni.
Ka ga wani gida can (yana nuna wani gida da ke gabansa)? To akwai mutum bakwai da suka mutu a gidan, wancan gidan kuma da kuke gani; shi ma akwai mutum guda bakwai da suka mutu a gidan. Haka zalika, akwai wata mata da ta mutu tana rike da dan jariri a jikinta, ni na shiga cikin gidan da kaina na cire shi a jikin uwar tana rike da shi a kirjinta, sai dai ita uwar ta rasu; amma jaririn na nan a raye.
Yanzu mene ne kokenku ko bukatarku ga gwamnati?
Muna bukatar gwamnati ta dube mu da idon rahama ta dauki dukkanin irin matakin da ya dace, domin kuwa mu dai ba za mu tashi daga wannan kauye ba, muna nan zama daram. Sannan kuma, ‘yan ta’adda; sun sha zuwa wannan kauye suna kashe mana mutane tare da sace su, har sai mun biya kudin fansa ka a kai ga sakin su.
A shekarun baya, sun kashe mana mutum hudu; amma wannan bai sa mun tashi daga wannan gari ba, sannan babu dama iyalanmu su tafi gona, domin cire amfani ba tare da sun far musu ba, saboda haka garinmu ba daji ba ne. Akwai lokacin da suka turo tumakinsu cikin garin nan yaranmu suka mayar musu da su, saboda ba namu ba ne. Har ila yau, hatta mabiya addinin Kirista da muka gayyata suka halarci wannan taron Maulidi, su ma sun rasa nasu rayukan.
Source: LEADERSHIPHAUSA