Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin Jihar Ogun ya rasu ana tsaka da atisaye a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
Rahotanni sun ce dan wasan yana atisaye da wasu ‘yan wasan kwallon kafa a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru.
Lokacin da abokan wasansa suka ga matashin mai shekaru 34 a duniya ya fadi, sai suka garzaya da shi asibitin jihar da ke Ijebu-Ode.
Sai dai duk da irin kokarin da kwararrun asibitin suka yi, an tabbatar da rasuwarsa a ranar da aka kai shi asibitin.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola, a ranar Talata ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa, dan uwan marigayin, Ganiyu Adebisi, ya karbi gawar matashin don birne ta.
“Dan uwansa ya zo ne ya kai rahoton faruwar lamarin a sashenmu na Igbeba. Iyayensa sun ce ba sa son wani bincike kuma suna son a birne marigayin kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar, ”in ji Odutola.
A wani la labarin na daban ranar Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 28, wanda ya gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Baya ga halartar taron, shugaban ya gana da Sarki Charles na Ingila, da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, da shugabannin kasashe da dama.
Har ila yau, shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kara kaimi tsakanin Nijeriya da Jamus domin inganta wutar lantarki a Nijeriya, ya kuma shirya wani babban taro tare da masu ruwa da tsaki da masu zuba jari kan kasuwanci a Nijeriya da shirin kaddamar da motocin bas amfani da wutar lantarki.
A ranar 29 ga watan Nuwamba, 2023, Tinubu ya bar Abuja zuwa Dubai domin halartar taron da ake sa ran kammalawa a ranar 12 ga watan Disamba, 2023.
Gwamnatin Tinubu ta sha suka kan wakilai 1,411 da Nijeriya ta tafi da su domin halartar taron, amma gwamnatin ta ce mutane 422 ne kawai ta tura domin halartar taron.
Source: LEADERSHIPHAUSA