Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar ta sanar da soke ƙawancen sojan kasar da Ƙungiyar Tarayyar Turai a ranar Litinin, inda ta janye izinin da ta bayar na wani shirin kungiyar EU da aka kafa domin ƙarfafa jami’an tsaro.
An kaddamar da shirin EUCAP Sahel Niger a shekarar 2012 domin taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙar ƴan bindiga da sauran barazana.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Niger ta sanar da soke ƙawancen sojan kasar da Ƙungiyar Tarayyar Turai a ranar Litinin, inda ta janye izinin da ta bayar na wani shirin kungiyar EU da aka kafa domin ƙarfafa jami’an tsaro.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawagar kasar Rasha ta gana da shugabannin mulkin sojin Nijar a birnin Niamey ranar Litinin, inda kasashen biyu suka amince da ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa alaƙar soji tsakaninsu.
An kaddamar da shirin EUCAP Sahel Nijar a shekarar 2012 domin taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙar ƴan bindiga da sauran barazana.
Kusan mutanen Tarayyar Turai 120 ake jibge a can na dindindin, kamar yadda shafin intanet na EUCAP ya bayyana.
Ita ma gwamnatin sojin Niger da ta karbi mulki a watan Yuli, ta buƙaci sojojin Faransa da ke taimakawa wajen yaƙar masuikirarin jihadi da su fice daga kasar.
Yarjejeniyar soji da Rasha
A ranar Litinin din ne kuma wata tawagar kasar Rasha karkashin jagorancin mataimakin ministan tsaronta suka gana da shugabannin mulkin soji na Nigar a babban birnin kasar Niamey, inda hukumomin Nijar suka ce ƙasashen biyu sun amince da ƙarafafa dangantalar soji tsakaninsu.
Wannan ziyarar dai ita ce ziyarar aiki ta farko da wani mamba na gwamnatin Rasha ya kai tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yuli, lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula lamarin da ya janyo suka daga kasashen duniya.
Tawagar, karkashin jagorancin Kanar-Janar Yunus-Bek Yevkurov ta samu tarba ne domin tattaunawa da shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani.
Ƙasashen “sun sanya hannu kan takardun ƙarfafa haɗin gwiwar soji tsakanin Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Rasha,” a cewar hukumomin Nijar.
Source: LEADERSHIPHAUSA