Jama’a da dama da masu fashin bakin lamurran yau da kullum na ganin hukunce- hukuncen shari’ar zaben 2023 sun zo da sabon salo ta yadda mafi yawa ke ganin kujerun jam’iyyun adawa ne kotuna suka fi karbewa akasin na jam’iyya mai mulki musamman ganin dukkaninsu daga yankin Arewa suke.
Ya zuwa yanzu tuni gwamnonin da ke kan mulki wadanda kujerunsu ke rawa da wadanda ke ganin su ne suka samu nasara a zabe, suka garzaya kotun koli domin raba gardamar karshe.
Shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da ke kan mulki da tsohon mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna na APC ce ta fi daukar hankalin al’ummar ciki da wajen kasar nan wadanda ba su yi kasa a guiwa ba wajen bayyana mabambantan ra’ayoyinsu kan adalci ko rashin adalcin hukuncin alkalan kotun farko da ta biyu da rudanin da ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara.
Gwamna Abba wanda aka fi sani da Abba gida-gida ya samu cikas ne a kotun sauraren karar zabe wadda a hukuncinta a ranar 20 ga Satumba ta saukar da shi kujerarsa bayan zabtare masa kuri’a dubu 165, 000 tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zabe.
Haka ma kotun daukaka kara a ranar 17 ga Nuwamba ta tabbatar da hukuncin farko ta kuma bayyana gwamnan a matsayin wanda ba shi da rajista da jam’iyyar NNPP, don haka a cewarta bai ma halarta ya shiga zabe ba ballantana a zabe shi.
Shari’ar zaben gwamna ta biyu da kallon ta zai koma sama a kotun koli ita ce shari’ar zaben Gwamnan Jihar Filato tsakanin Gwamna Caleb Muftwan na PDP da dan takarar Gwamna na APC Nentawe Yilwatda. Kotun farko dai ta tabbatar da zaben gwamnan a yayin da kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun farko ta kuma tabbatar da dan takarar na APC a matsayin wanda ya lashe zabe da halastattun kuri’u a ranar 19 ga Nuwamba.
Shari’ar Filato wadda kotun daukaka kara a karkashin jagorancin mai shari’a Elfrieda Williams- Dawodu ta yanke ta bayyana cewar gwamnan ba dan jam’iyyar PDP ba ne. A cewar alkalan, dan takarar APC ya yi nasara ne saboda batun tsayar da dan takara lamari ne da ya shafi kafin da bayan zabe, akasin hukuncin kotun sauraren korafe korafe zabe wadda ta bai wa gwamnan nasara. Kotun ta ce ta aminta da hujjojin mai kara kan gazawar PDP wajen gudanar da sahihin zaben shugabannin jam’iyya
Hakazalika, Kotun Daukaka Kara a Abuja, a ranar 23 ga Nuwamba ta tabbatar da zaben Gwamnar Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ta hanyar soke hukuncin kotun sauraren karar zabe da ke Lafiya wadda ta bai wa dan takarar jam’iyyar PDP, Dabid Ombugadu nasara a ranar 2 ga Oktoba.
Hukuncin na Nasarawa ya kara haifar da suka ga bangaren shari’a ta yadda abokan hamayya suka fito fili suka bayyana cewar dama can sun fada akwai lauje cikin nadi a hukunce- hukuncen da kotunan ke yi tare da kara kafa hujja da jihar wadda jam’iyya mai mulki ta hango za ta koma hannun jam’iyyar adawa.
A ranar 19 ga Nuwamba kuwa, kotun daukaka kara ta soke hukuncin da kotun sauraren karar zabe da ke Sakkwato ta yanke wadda ta tabbatar da nasarar lashe zaben Gwamna Dauda Lawal na jam’iyyar PDP. To amma hukuncin kotun daukaka kara ya zo wa jama’a da mamaki domin kuwa kotun ta tsige gwamnan tare da bayar da umarnin a sake gudanar da sabon zabe a kananan hukumomi uku, wato Maradun, Bukkuyum da Birnin- Magaji. Kasancewar Zamfara jihar PDP, wasu na ganin zargin da ‘yan adawa ke yi na siyen hukunci ya kara fitowa fili.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan kace- nacen jama’a kan hukunce- hukuncen da kotuna suka yi; Alkalin Alkalai na Kasa, Olukayode Ariwoola ya bayyana cewar barazanar masu tayar da zaune tsaye ba za ta yi tasiri gare su har ta sa su kauce ga hukunce hukuncensu ba.
A jawabinsa a wajen taron sabuwar shekarar fannin shari’a ta 2023/2024, ya bukaci alkalai da su jajirce tare da sadaukar da kai da kuma zama masu gaskiya da adalci ga shari’un da ke gaban su ta hanyar kare kima da darajar da aka san fannin shari’a da su.
Ya ce a yayin gudanar da aiki yana da kyau alkalai su rika aiki tukuru tare da mutunta masu kara da shaidu da lauyoyi tare da yin kas-kas da kai a ikon da suke da shi.
Ya ce a kodayaushe, doka dai doka ce, ko muradin wa ta shafa, abin da ke a gaban su a matsayin alkalai shi ne bayyana gaskiya da adalci Ya ce ka da alkalai su taba damuwa da amon muryoyin masu ta da zaune tsaye, su tsaya su yi aikin su bisa ga tanadin doka.
Jigo daga cikin jiga- jigan PDP da suka tofa albarkacin bakinsu kan hukunce-hukuncen kotunan zabe a kasar nan shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda karara ya bayyana cewar a bisa ga yadda alkalai ke zartas da hukunci a kotuna, tsarin dimokuradiyyar kasar nan na cikin garari.
Abubakar wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa kan yada labarai, Paul Ibeh ya bayyana cewar jam’iyyar APC tana amfani da bangaren shari’a ne domin murkushe jam’iyyun adawa. Ya bayar da misali da hukunce hukuncen da kotunan daukaka kara suka zartas kwanakin baya wato Zamfara, Filato, Kano da Nasarawa wadanda ya ce Gwamnatin Tinubu na labewa da shari’a ta na bai wa jam’iyyar APC nasara.
Wazirin Adamawa ya bayyana cewar, a bayyane APC ke amfani da magudi tare da fakewa da bangaren shari’a wajen soke nasarar abokan hamayya a wasu jihohi wanda ya ce hakan ba komai ba ne illa kokarin murkushe dimokuradiyya.
Ya bayyana cewar dimokuadiyyar Niijeriya tana da cikin halin rai-kwakwai- mutu- kwakwai a karkashin mulkin jam’iyyar APC a yayin da tsarin shari’a da aka sani da kima da martaba a baya, a yanzu kotuna sun zama ana siyar da hukunci kudi-hannu.
“Abin damuwa ne matuka, abin da yake faruwa a shari’ar zaben Gwamnan Filato tabbaci ne na barazanar da dan majalisar APC ya yi a faifan bidiyo da ya yadu cewar jam’iyya mai mulki za ta murde shari’ar domin samun nasara a kotuna.
Atiku ya ce ya yi mamakin yadda Lagas a inda Shugaba Tinubu ya fito a matsayin ubangida, jam’iyyun adawa suka zama abin kyama, kowa da kowa ciki har da alkalai an tilasta masu shiga jam’iyyarsa.
A tsokacin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya nuna rashin jin dadi yadda wasu tsirarun alkalai uku zuwa hudu ke zartas da hukunci a kasar nan ta yadda suke iya soke zabin da miliyoyin jama’a suka jefa wa kuri’a.
Obasanjo wanda ya yi bayani a Abeokuta a wani taron sake fasalin dimokuradiyya yana magana ne kan hukuncin da kotunan daukaka kara suka zartas kan zaben gwamnoni a inda ya nuna akwai bukatar sake bitar karfin ikon alkalai na canza zabin miliyoyin jama’a.
A cewarsa tsarin mulkin dimokuradiyya a kasashen yamma ba zai taba tafiya daidai da ra’ayin al’ummar yankinmu ba kasancewar ba ya la’akari da ra’ayin mafi yawan al’umma wadanda su ne kashin bayan dorewar mulkin dimokuradiyya.
Kungiyar Dattawan Arewa tana kan gaba cikin kungiyoyin da suka nuna takaicin yadda hukuncin shari’ar zaben Kano ya kasance ta yadda hukuncin da aka zartas a kotu daban kuma rubutaccen hukuncin da aka bai wa masu ruwa da tsaki a shari’ar daban.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya ce abin damuwa ne kwarai yadda lamarin ya zo da rudarwa wanda barazana ne ga makomar dimokuradiyya.
Ya ce wannan abin da ya faru zai iya tabbatar da kalamai da damuwar da tsohon alkalin kotun koli, Musa Dattijo ya nuna kwanan baya a jawabinsa a taron bankwana bayan kammala aikin shari’a a inda ya ce cin hanci da karan tsaye sun yi katutu a fannin shari’a.
Kungiyar Dattawan Arewan ta jaddada muhimmamcin da ke akwai na samun ingantaccen tsarin shari’a da zai kwatanta gaskiya da adalci wajen aiwatar da doka da tabbatar da dimokuradiyya.
“Fannin shari’a na taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da gaskiya, kare ‘yancin ‘yan kasa da tabbatar da kimar tsarin zabe. Duk wani abin da zai yi wa wadannan ginshikan zagon kasa, to ya gurbata tubalin ginin dimokuradiyya.”
Shugaban Cocin Katolika na Sakkwato kuma wakili a kwamitin canza fasalin shari’a na Lawal Uwais, Bishop Mathiew Hassan- Kuka ya bayyana cewar fannin shari’a a Niijeriya sun sa kansu a cikin siyasa kamar yadda ya bayyana a wani taro kan sha’anin shari’a a Kaduna.
Kuka ya bukaci bangaren shari’a da su dawo da kima da martabar da aka san su da ita ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci ba tare da sani ko tsoro ba. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ka da su cire tsammani domin za a samu kyakkyawar makoma.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani a yayin tofa albarkacin bakinsa kan sakamakon shari’ar Kano, bayyana cewar ya zama tilas a yi taka- tsan- tsan kan sahihan takardun rubutaccen hukuncin kotun daukaka kara wanda a bayyane ya baiwa Abba Kabir nasara.
Ya ce ba za a samu nasara a dorewar dimokuradiyya a Niijeriya ba idan har son zuciya zai rika danne abin da doka ta tanada, don haka ya ce ya zama wajibi a kawar da son rai domin lamarin tamkar gurneti ne.
A martanin fadar shugaban kasa kan ikirarin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kan sayar da hukunci ta bukaci tsohon dan takarar na PDP ya san irin kalaman da zai rika yadawa.
Fadar ta ce ya zama wajibi Atiku Abubakar ya iya bakinsa domin babu komai a kalamansa face kokarin zubar da kimar fannin shari’a a kokarin cimma burin siyasarsa
Martanin fadar wanda ya fito daga bakin mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ta bayyana cewar Shugaba Tinubu yana mutunta tsarin dimokuradiyya, don haka ba zai sa baki kan hukuncin da alkalai suka zartas ba.
Ya zuwa yanzu daiu kallo ya riga ya koma kan kotun koli domin ganin yadda za ta kaya a shari’un zaben gwamnonin da suka tayar da kura. Shin hukunce- hukuncen za su tabbatar da kima da martabar fannin shari’a ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci ko kuwa a’a zargin da jama’a suke yi na siyar da hukunci zai tabbata? Lokaci kadai zai tabbatar.
Source: LEADERSHIPHAUSA