Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga majalisar dokokin Nijeriya.
Kasafin kudin na shekarar 2024, wanda ya kunshi sama da Naira tirliyan 27.5 zai mayar da hankali wajen karfafa tsaron kasa da samar da aikin yi da harkokin zuba jari da rage fatara a tsakanin al’umma.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum.
Kazalika za ake canjar da dalar Amurka daya a kan canjin Naira 750.
Kasafin kudin ya yi kudurin kashe Naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum.
Sai kuma Naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka.
A wani labarin na daban gwamnatin Tarayya ta ce tana kashe Naira miliyan uku a kullum wajen ciyar da fursunoni 4,000 da ke gidajen yari a fadin kasar nan.
Amma al’amarin ya sanya ta dole rage yawan fursunonin da ke daure a gidajen yari.
Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo bayan shigarsa ofis a watannin baya, ya rage cunkoson fursunoni a gidajen yari a kasar.
A cewar ministan, akwai fursunoni 80,804 a gidajen yari 253, wanda ciyar da fursunonin ke daukar kaso na kudi daga asusun gwamnatin tarayya.
“Ciyar da wadannan fursunoni 4,068 na salwantar da kusan Naira miliyan uku a kullum. Idan aka hada adadin miliyan uku zuwa kwana 365 nawa za a samu?,” in ji shi.
Kafin a fara aikin rage cunkoson fursunonin, ministan ya ce ana bukatar Naira miliyan 500 domin biyan tarar fursunonin da ke daure.
Ko da yake kalaman nasa sun janyo cece-kuce da lauyan kare hakkin bil adama Femi Falana ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba shirin sakin fursunonin.
Sai dai Olubunmi ya ce an tara kudaden ne daga kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce tunda ba gwamnati ce kashe kudin tarar fursunonin ba, ya dace a ci gaba da aikin rage cunkosonsu a gidajen yari.
Ministan ya ce, “Mun tara Naira miliyan 585 daga kamfanoni masu zaman kansu don biyan tarar domin ceton gwamnati daga kashe makudan kudade, ”in ji shi.
Source: LEADERSHIPHAUSA