Kasurgumin dan daba da aka fi sani da Hantar Daba wanda rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ke nema ruwa a jallo ya mika kansa ga rundunar.
Hantar Daba ya mika kansa ga hedikwatar ‘yansanda da ke Kano a ranar Litinin.
Idan ba a manta ba Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mohammed Usain Gumel ya sanar da cewa watanni biyu da suka gabata za a fara aiwatar da shirin tabbatar da tsaro a Jihar Kano ta hanyar yakar ‘yan daba.
Da yawa daga cikin ‘yan daba a jihar sun mika wuya ga ’yansanda yayin da Hantar Daba ya tsere kuma daga baya aka bayyana cewa ana neman sa ruwa a jallo.
Sai dai a wata sanarwa da rundunar ‘yansandan ta raba wa manema labarai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yansandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a ranar Talata, ya ce Hantar Daba, wanda ya gudu, ya mika kansa ga rundunar ‘yansandan.
“Abin farin ciki shi ne, mutum na karshe; Hantar Dabaa a jiya 27 ga watan Nuwamba, 2023 wanda ya tsere daga karshe ya mika kansa ga rundunar ‘yansanda.
“Ya yi matukar nadama da irin mummunar rayuwar da ya yi a baya, kuma a yanzu a shirye yake ya taka rawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar.
“A halin yanzu, Hantar Dabaa yana hannun rundunar ‘yansandan Jihar Kano,” in ji sanarwar.
Source: LEADERSHIPHAUSA