Akwai fargabar karin mutane za su iya mutuwa sakamakon cututtuka fiye da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza idan ba a kai agaji bangaren lafiya na kasar ba, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar.
“A hankali za mu ga karin mutane suna mutuwa daga cututtuka fiye da hare-hare idan ba mu gyara tsarin lafiya ba,” kamar yadda Margaret Harris ta bayyana, mai magana da yawun WHO.
Ta bayyana cewa rufewar asibitin Al Shifa da ke arewacin Gaza a matsayin “bala’i” inda ta bayyana damuwarta kan ci gaba da tsare wasu daga cikin jami’anta da dakarun Isra’ila suke yi.
0800 GMT — Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe Gabar Yamma da Kogin Jordan
Harbin da sojojin Isra’ila suka yi ya kashe Bafalasdine na biyu a kusa da birnin Ramallah a Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Majiyoyi daga Asibitin Gwamnati na Salfit sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, “An kawo wani mutum daga garin Kafr Ayn na arewa maso yammacin Ramallah sashen kula da marasa lafiya na gaggawa dauke da ciwuka na harbin bindiga mai muni, kuma ya mutu.”
Hukumomi a garin na Kafr Ayn sun ce “wasu sojojin Isra’ila sun je garin inda suka kama mutumin, abin da ya kai ga arangama tsakaninsu da gomman Falasdinawa.”
Ganau sun bayyana cewa “sojojin sun harba harsasai kan mutane abin da ya jikkata Malik Al Barghouthi bayan harsasai uku sun same shi. Daga nan ne aka kai shi Asibitin Gwamnati na Salfit, inda aka sanar da rasuwarsa.
A wani labarin kuma, dakarun Isra’ila sun kashe wani Bafalasdine ranar Litinin da maraice a Yammacin birnin Ramallah da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe Gabar Yamma da Kogin Jordan ya karu zuwa 242 tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma’aikatar lafiya.
0639 GMT — Har yanzu akwai kusan Falasdinawa ’60 da ke gidan yarin Isra’ila’
Wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana cewa har yanzu akwai matan Falasdinawa 60 da ke gidan yarin Isra’ila tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Amal Sarahneh wadda jami’ar watsa labarau ce a kungiyar Palestinian Prisoners Society ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Isra’ila ta kama matan Falasdinawa 56 da mata a kame-kamen da suke yi a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudustun bayan 7 ga watan Oktoba inda suka kama mutum 3,260.
Sarahneh ta kara da cewa Isra’ila ta saki Falasdinawa mata 33 karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas a kwanaki hudu da suka gabata.