Majiyoyin labarai sun ba da rahoton harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a yankuna daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan da kuma kame Falasdinawa da suke yi.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya bayar da rahoton cewa, a yayin da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ta shiga kwana na hudu, majiyoyin labarai sun ba da rahoton harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a yankuna daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan tare da kame Falasdinawa masu yawa.
Da sanyin safiyar yau ne dakarun yahudawan sahyuniya mamaya suka kai farmaki a yankin “Bani Naim” dake gabashin Hebron da kuma kauyen Kafarnameh dake yammacin Ramallah tare da kame kusan Palastinawa 50.
Sojojin yahudawan sahyoniya sun kuma kai hari a sansanin “Askar” da ke gabashin Nablus da yankin “Jaba” a kudancin Jenin.
Majiyoyin Falasdinawa sun jaddada cewa sojojin Isra’ila na kame Falasdinawa da dama a yankin.
Idan dai ba a manta ba, a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin mayakan Falasdinawa a yammacin kogin Jordan, an fara tsagaita bude wuta na kwanaki hudu tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a zirin Gaza da karfe 7:00 na safiyar Juma’a (lokacin gida) zuwa yanzu an kammala matakai 3 na musayar fursunoni tsakanin bangarorin.

Eouy: ABNAHAUSA