Ya zuwa yanzu dai na hada wannan rahoton dayawa daga cikin wadanda aka saki din sun isa zuwa ga iyalansu inda suke ta murna da farinci akan kokarin da Hamas ta yi kuma take yi na ganin an sake sauran Falasɗinawa da yanar da Falasdinu daga mayar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: An saki fursunonin Falasdinawa 39
Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran -IRNA- ya bayar da rahoto cewa Ma’aikatar kula da fursunonin Falasdinu a daren Juma’a ta tabbatar da cewa sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun sako fursunoni 39.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera Qatar da Urdun cewa, ma’aikatar harkokin fursunonin Palasdinu ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, wannan tawagar ita ce rukunin farko na fursunonin Palasdinawa da aka sako da yammacin yau bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Majiyoyin labarai sun sanar da cewa wadannan fursunoni sun kasance mata 24 ne da kananan yara 15.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta kuma sanar da cewa jami’an gidan yari na sahyoniyawan sun dauki matakan da suka dace domin sakin wadannan fursunonin.
A ‘yan sa’o’i da suka gabata ne aka bayyana sunayen wadannan mutane 39, kuma an ce an kai wadannan fursunonin zuwa gidan yarin Ofer Barrack kuma za a sake su bayan haka.
Shugaban sashen kula da harkokin fursunonin Falasdinu ya sanar a baya cewa za a mika wadannan fursunonin ga kungiyar agaji ta Red Cross.
Ya ce masu shiga tsakani su ne ke tabbatar da yarjejeniyar musayar fursunoni.
Shugaban Sashen Harkokin POW ya lura cewa: Muna fatan Qatar, Masar da Amurka za su ci gaba da kokarin sakin dukkan fursunonin.
Ya zuwa yanzu dai na hada wannan rahoton dayawa daga cikin wadanda aka saka din sun isa zuwa ga iyalansu inda suke ta murna da farinci akan kokarin da Hamas ta yi kuma take yi na ganin an sake sauran Falasɗinawa da yanar da Falasdinu daga mayar Isra’ila.
Source: ABNAHAUSA