Sojojin Isra’ila na ci gaba da kama mutane a Gabar Yammacin Kogin Jordan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Isra’ila ta kashe Falasdinawa 14, 854 a hare-haren da ta kwashe kwana 49 tana kaiwa a Gaza.
Fiye da Falasdinawa 7,000 sun bata ko kuma an binne su a cikin baraguzan gine-gine, a cewar hukumomi.
Isra’ila ta gargadi dubban Falasdinawa da suka samu mafaka a kudancin Gaza da kada su yi yunkurin komawa gidajensu a arewaci.
1041 GMT — Dakarun Isra’ila sun harbe wasu Falasdinawa
Dakarun Isra’ila sun harbe wasu Falasdinawa biyu sannan suka jikkata mutum 11 a yayin da suka nufi arewacin Gaza duk da gargadin da Isra’ila ta yi na kada su yi hakan.
Wani dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ga gawawwakin mutanen biyu da kuma wadanda suka jikkata a yayin da aka kai su asibitin Deir al Balah da ke kudancin Gaza. An harbi mutanen da suka jikkata ne a kafafunsu.
An ga daruruwan Falasdinawa suna kokarin tafiya arewacin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana hudu ta soma aiki.
Ganau sun ce dakarun Isra’ila suna bude wuta a kan mutanen da suka yi kokarin tafiya arewacin Gaza daga kudanci.
0746 GMT — Sojojin Isra’ila na ci gaba da kama mutane a Gabar Yammacin Kogin Jordan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Sojojin Isra’ila na ci gaba da kama mutane tare da kai samame a Yammacin Kogin Jordan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakaninsu da Hamas a Gaza wacce ta soma aiki da sanyin safiya.
A cewar wani mai aiko da rahotanni ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu da ke yankin, rundunar sojin Isra’ila ta kai samame a birane da garuruwa da dama a Gabar Yammacin Kogin Jordan inda ta kama Falasdinawa da yawa.
A gefe guda, wasu majiyoyi na hukumomin lafiyar Falasdinawa sun shaida wa Anadolu cewa dakarun Isra’ila sun jikkata akalla Bafalasdine guda loacin da suka kai hari a Tsohon Birni da ke Birnin Nablus.
Kazalika ganau sun ce dakarun Isra’ila sun tsare Falasdinawa biyu a samamen da suka kai Nablus. Dakarun Isra’ila sun kona motoci biyu na Falasdinawa kafin su janye daga yankin.
0016 GMT — Shugaban Cuba ya shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba ya jagoranci gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a yayin da Isra’ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza.
Masu gangamin sun rika daga tutocin Falasdinu inda suka caccaki Amurka bosa goyon bayan da take bai wa Isra’ila.
Ma’aikatar Cikin Gida ta kasar ta wallafa sako a shafin X cewa mutum sama da 100,000 sun shiga zanga-zangar.
Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa./Hoto: Reuters
0500 GMT — Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta soma aiki
Yarjejeniyar kwana hudu game da yakin da Isra’ila take yi a Gaza ta soma aiki inda za a yi musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu, a wani mataki na farko na samun sauki tun bayan yakin da ya barke makonni bakwai da suka gabata.
Bayan an dade ana tattaunawa kan tsagaita wuta, yarjejeniyar ta soma aiki da misalin karfe 7 na safe a agogon yankin wato karfe 5 a agogon GMT, inda aka ji saukin rugugin bindigogi tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.
Bayan tsagaita wutar, za a saki kashin farko na fursunoni 13 da ake tsare da su a Gaza, da kuma wasu fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar kasar Qatar wadda ita ce take shiga tsakani.
Wannan tsagaita wuta za ta kawo sauki ga mutum fiye da miliyan biyu da ke Gaza, wadanda suka yi ta fuskantar hare-haren Isra’ila, lamarin da ya kashe fiye da mutum 14,500 da raba dubbai daga muhallansu.
Source: TRThausa