Bayan kusan kwanaki 50 na yaki a Gaza, an fara tsagaita wuta na wucin gadi na kwanaki 4.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Bayan kusan kwanaki 50 na yaki a Gaza, an fara tsagaita wuta na wucin gadi na kwanaki 4.
Ya kamata a saki fursunonin Isra’ila 50 kuma ga kowane fursunonin Isra’ila, za a saki mata da yara Falasdinawa 3.
A wani labarin na daban sanarwar tsagaita wuta a kwanaki 4 a Gaza da kuma musayar fursunoni Hamas: An shirya rubutun yarjejeniyar ne bisa bukatar gwagwarmaya
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu Hamas ta fitar da bayaninta dangane da wannan yarjejeniya kamar haka:
Mun cimma yarjejeniya kan tsagaita bude wuta na jin kai na kwanaki hudu. Daruruwan manyan motoci na musamman da za su kai kayan agaji da mai za su isa dukkan yankunan Gaza ba tare da togiya ga arewa da kudanci.
Dakatar da yaki daga bangarorin biyu, da ayyukan soji na sojojin yahudawan sahyoniya a dukkanin yankunan Gaza, da kuma zirga-zirgar motocin sulke na wannan gwamnati a Gaza.
Mata da yara 50 na Isra’ila ‘yan kasa da shekaru 19 za a sake su a kan mata da yara Falasdinawa 150 da ke kasa da shekara 19 bisa ga bayanan da aka yi garkuwa da su.
A yayin da muke sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, muna jaddada cewa, hannayenmu za su ci gaba da kasancewa a kan turba kuma bataliyoyinmu masu nasara a shirye suke don kare al’ummarmu da kuma fatattakar makiya.
Kamar Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ofishin Netanyahu na cewa wannan gwamnati ta kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Bisa wannan yarjejeniya, za a sako mata da yara 50 cikin kwanaki 4, inda za a tsagaita tafka yaki.
Hamas ta kuma sanar da cewa: Bayan tattaunawa mai wahala da sarkakiya, sun sanar da cewa sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki 4. Bisa wannan yarjejeniya, an dakatar da duk wani matakin soji na bangarorin biyu, sannan za’a saki mata da kananan yara 50 na Isra’ila mamadin sakin mata da kananan yara Palasdinawa 150.
Har ila yau, bisa wannan yarjejeniya, za a aike da daruruwan tireloli na agajin jin kai, da magunguna da man fetur zuwa dukkan yankunan zirin Gaza kamar yadda aka shardanta a yarjejeniyar.
Bugu da kari, za a dakatar da zirga-zirgar motocin soji na ‘yan mamaya zuwa zirin Gaza da kuma jirgin mayakan. Inda ‘yan mamaya su kai alkawarin ba za su kai hari ko kama wani ba.
An tsara tanade-tanaden yarjejeniyar daidai da ra’ayin ‘yan gwagwarmaya ne, wadanda manufarsu ita ce yi wa al’umma hidima da kuma karfafa zaman lafiyarsu daga wuce gona da iri.
Yayin da muke shelanta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, muna jaddada cewa hannunmu na kan aiki na lura da abunda zai faru nan gaba.
Source: ABNAHAUSA