Yarjejeniyar kwana hudu game da yakin da Isra’ila take yi a Gaza ta soma aiki inda za a yi musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu, a wani mataki na farko na samun sauki tun bayan yakin da ya barke makonni bakwai da suka gabata.
Bayan an dade ana tattaunawa kan tsagaita wuta, yarjejeniyar ta soma aiki da misalin karfe 7 na safe a agogon yankin wato karfe 5 a agogon GMT, inda aka ji saukin rugugin bindigogi tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.
Bayan tsagaita wutar, za a saki kashin farko na fursunoni 13 da ake tsare da su a Gaza, da kuma wasu fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar kasar Qatar wadda ita ce take shiga tsakani.
Wannan tsagaita wuta za ta kawo sauki ga mutum fiye da miliyan biyu da ke Gaza, wadanda suka yi ta fuskantar hare-haren Isra’ila, lamarin da ya kashe fiye da mutum 14,500 da raba dubbai daga muhallansu.
0420 GMT — Isra’ila ta kai hari wata makarantar MDD, ta kashe mutum 300 da jikkata 100
Akalla mutum 30 sun mutu sannan sama da mutum 100 sun jikkata sakamakon wani hari da Isra’ila ta kai a wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa a arewacin Gaza, a cewar kungiyar Hamas mai fafutukar kare hakkin Falasdinawa.
An kai harin ne a Makarantar Abu Hussein wacce hukumar UNRWA ke gudanarwa a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia, a cewar Hamas.
Rundunar sojin Isra’ila ba ta ce komai kan wannan batu ba.
Source: TRTHausa