Sanata mai wakiltar Mazabar Borno ta Tsakiya, Sanata Kaka Shehu Lawan ya ga batar da wani kuduri na gaggawa da ke neman tattara dokokin da aka yi a kasar nan a tsakanin shekara 19. gaban zauren Majalisar Dattawa da ke Abuja.
Majalisar Dattawa ta umarci Kwamitocinta na Shari’a da na ‘Yancin Dan’adam da na Dokoki ba tare da bata lokaci ba su fara shiri domin tattara dokoki da aka yi a kasar nan daga shekara ta 2004 zuwa shekara ta 2023 a tarasu guri daya.
Sanatan ya ce dalilin sa na gabatar da wannan Kuduri shi ne ya lura cewa kimanin shekaru 19 kenan da aka tattara dokokin kasar nan wanda hakan ya haifar da rudani a kasa inda ake amfani da dokoki daban-daban masu karo da juna.
Kaka ya kara da cewa ya lura cewa masu tallar littattafai a kan titunan suna dauke da kundin shari’a irin daban-daban a kasar nan; wanda hakan koma baya ne ga kasar.
Kotun Daukaka Kara Ta Ce Tuntuben Alkalami Aka Samu Wajen Rubuta Kundin Hukuncin Shari’ar Zaben Kano
Ya kara da cewa, ya lura Malaman Makarantu a Jami’a da Dalibai kai har ma da Lauyoyi su ma suna amfani da Kundin Dokokin na Kasar nan iri daban-daban wanda hakan bai da ce ba.
Sanatan ya ci gaba da cewa, tun wancan lokaci zuwa yanzu Majalisar Tarayya ta yi dokoki masu tarin yawa wadanda shugabannin kasa daban-daban sun saka musu hannu amma har ya zuwa yanzu ba a tattara wadannan dokoki ba guri guda domin amfanar ‘Yan Nijeriya.
Sanatan wanda ya kara wa mane ma labarai haske a ofishinsa ya ce doka ce ta sahale wa ofishin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da ya gabatar da wannan bukata ta tattara dokokin na kasa tare da hadin gwiwa da Majalisar Tarayya.
Ya kara da cewa idan aka har-hada wadannan dokoki guri guda zai taimaka wajen gudanar da shari’a a Nijeriya ba tare da kawo rudani ba. In da ya ce a halin yanzu tabbas akwai rudani a yadda ake yanke hukunce-hukunce a Kotunan Nijeriya sakamakon bambance – bambance da ake samu a Kundin Shari’a.
Source: LEADERSHIPHAUSA