Wani likita a Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza ya ce dakarun Isra’ila sun kama daraktan asibitin da wasu ma’aikatansa.
“An kama Dakta Mohammad Abu Salmiya tare da manyan likitoci da dama,” a cewar Khalid Abu Samra, shugaban bangarori na asibitin wanda yake tsaka da ce-ce-ku-ce a game da hare-haren da suka kaiwa a yankin.
Isra’ila ta kashe Dakarun Falasdinawa 14,532 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, daga cikinsu akwai mata fiye da 6,000 da kananan yara 4,000, a cewar hukumomin Falasdinu. /Hoto: Reuters
0422 GMT — Isra’ila ta kara kaimi wurin kai hare-hare a Gaza gabanin lokacin tsagaita wuta
Isra’ila ta kara kaimi wurin kai hare-hare a fadin Gaza gabanin lokacin tsagaita wuta da aka amince da shi tsakanin dakarunta da masu fafutuka na kungiyar Hamas ya soma aiki.
Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare a yankuna da dama na yankin da aka mamaye, musamman a arewacin Gaza, kamar yadda kafanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA ya rawaito.
Ya kara da cewa an kashe mutane da dama sakamakon hare-haren na sojojin Isra’ila a wasu gidaje da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat.
0334 GMT — Amurka ta kama wasu jiragen yaki marasa matuka da aka harba daga Yemen: Pentagon
Amurka ta kama wasu jiragen sama marasa matuka da aka harba daga yankunan da ke karkashin ikon Houthi a Yamen, in ji rundunar tsakiya, CENTCOM.
An harbo jiragen ne a lokacin da jirgin yakin Amurka ke sintiri a Tekun Maliya. Jirgin da ma’aikatan jirgin ba su lalace ko jin rauni ba, “in ji CENTCOM a shafin X.
0307 GMT — Biden ya ce Amurka ba za ta bari a tursasa wa Falasdinawa fita daga Gaza ba
Shugaban Amurka Joe Biden ya shaida wa takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi ta wayar tarho cewa kasarsa ba za ta amince a tursasa wa Falasdinawa fita daga yankin Gaza da aka mamaye ba, ko kuma Gabar Yammacin Kogin Jirdan, kamar yadda wata sanarwa daga Fadar White House ta bayyana.
“Shugaban kasa yana mai tabbatar da shirinsa na kafa kasar Falasdinawa da kuma jaddada muhimmancin rawar da Masar za ta taka wajen ganin an bi wadannan ka’idoji,” in ji White House.
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Biden ya bayyana jin dadinsa “game da kokarin Masar na kulla yarjejeniyar sakin mutanen da Hamas ta kama tare da tsagaita wuta a Gaza.”
Source: TRTHhausa