Kungiyar dalibai ta jami’ar koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (SUG) ta yaba da biyan kudin makaranta ga dalibai 308 da sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Sanata Aminu Iya Abbas, ya yi, ta ce sanatan ya cancanci yabo.
Shugaban kungiyar, Kyauta Samuel Tari ne ya bayyana haka a Yola, inda ya ce, “Biyan kudin makaranta ga dalibai a wannan mawuyacin hali da ake ciki, babban karfafa guiwa ne ga matasa.
“Tallafawa harkar ilimi, kamar kawar da halin lalacewa ne a tsakanin matasa, zai kuma taimaka wa Matasan yankin ta hanyar ci gaba da karatu ba tare da matsala ba.”
Tunda farko, acikin wata sanarwa da mai taimakawa Sanata kan harkokin kafafen sadarwa Muhammad Ahmad ya fitar, ya ce, Sanata Iya Abbas, wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire (Science, Technology and Innovation) ya biya kudin makaranta ga dalibai 308.
Sanarwar ta ce, Sanata ya dauki matakin ne biyu bayan halin kunci da wahalhalun da daliban suka tsinci kansu na gaza biyan kudin makarantar. Biyan kudin zai taimaka wa daliban damar kammala karatunsu da samun ilimi ingantacce.
Daliban da suka ci gajiyar tallafin sun futo ne daga kananan hukumomin Fufore dalibai 14, Yola ta arewa 87, Yola ta kudu 61, Girei 36, Song 25, Hong 59 da kuma Gombi 26.

Source: LEADERSHIPHAUSA