Quds (IQNA) Falasdinawa masu ibada sun gudanar da sallar asuba da juma’a a titunan birnin Kudus bayan da yahudawan sahyuniya suka hana su shiga masallacin Al-Aqsa a mako na shida a jere.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Arabi al-Jadeed cewa, daruruwan Palasdinawa ne suka gudanar da sallar asuba da juma’a a titunan da ke kusa da tsohon birnin na gabacin birnin Kudus bayan da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka hana masu ibada isa masallacin Aqsa domin gudanar da sallar.
A ranar Juma’a ta shida a jere, ‘yan sandan Isra’ila sun sanya takunkumi mai tsauri kan shiga masallacin, wanda ya ba da dama ga tsofaffi kawai su yi salla.
Tun lokacin da aka fara yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba (Operational-Aqsa Storm a ranar 25 ga watan Oktoba), sojojin Isra’ila sun sanya dokar hana shiga masallacin, amma suna tsananta wannan takunkumi a ranar Juma’a.
Domin hana Falasdinawa isa masallacin Al-Aqsa, ‘yan sandan Isra’ila sun kafa shingaye a mashigin tsohon birnin da ke gabashin birnin Kudus, kuma tsofaffi ne kawai aka bari su wuce.
Har ila yau sojojin yahudawan sahyuniya sun kafa shingayen binciken ababen hawa a kofar masallacin Al-Aqsa da ke bayan birnin Quds.
Daruruwan masu ibada ne suka gudanar da sallar asuba da Juma’a a titunan da ke kusa da masallacin Al-Aqsa, ciki har da Wadi Al-Jawz da titin Salahuddin.

Source: IQNAHAUSA