Washington (IQNA) Wata fitacciyar mai fafutuka a dandalin sada zumunta na Tik Tok wadda ta musulunta kwanan nan bayan abubuwan da suka faru a Gaza ta ce ta yi sha’awar karatun kur’ani a karkashin tasirin labaran yakin da ake yi a wannan yanki da kuma sanin sirrin tsayin daka da gwagwarmaya na mutanen Gaza.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Gulf 365 cewa, ‘yar fafutuka ba’amerika Megan Rice, wacce labarin yakin Gaza da zalunci da tsayin daka na Palastinawa ya yi tasiri a kanta ta musulunta, ta yi bayani kan yadda ta fara sha’awar karatun kur’ani.
Ita daya ce daga cikin fitattun fuskokin Tik Tok, ta sanar a wani shirin kai tsaye daga shafinta sanye da hijabi cewa ta samu goron gayyata na halartar wani bikin Musulunci da za a yi nan ba da dadewa ba a birnin Chicago.
A farkon abubuwan da suka faru a Gaza, Megan Rice ta sadaukar da asusunta don kare al’ummar Palasdinu tare da bayyana rashin adalcin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi musu.
A wani faifan faifan bidiyo da take kuka ga Falasdinawa da aka kashe, ta ce ta yi mamakin irin tsayin dakan da Falasdinawa suka yi a cikin wannan mawuyacin hali.
Ta ce za ta so sanin sirrin tsayin daka da kuma karfin imaninsu dangane da kisan kiyashin da suke fuskanta. Wasu sun ce hakan ya faru ne saboda tsananin imaninsu da Allah da kuma abin da aka ambata a cikin Alkur’ani mai girma. Saboda haka, Meghan ta yanke shawarar karanta Al-Qur’ani da bincike kan mahangar Al-Qur’ani.
Karatun Alqur’ani ya burge Meghan kuma ya motsa ta. Tana cewa: Na yi sha’awar ganin ko akwai audio na Alqur’ani mai girma ko babu sai na fara saurare. Bayan karanta Alqur’ani, sai na gane cewa sakon wannan littafi a sarari yake.
Source: IQNAHAUSA