Rikicin da ke kara ta’azzara a kan iyakar Lebanon da Isra’ila ka iya zama gagarumi
Rikicin da ke kara ta’azzara a kan iyakar Lebanon da Isra’ila ka iya zama gagarumi
Ya zuwa yanzu, sama da ‘yan kungiyar Hizbullah 70 da fararen hula 10 aka kashe a kasar Lebanon, sannan an kashe mutane 10 da suka hada da sojoji bakwai a Isra’ila.
Harin na Isra’ila ya kashe mutum biyu a kudancin Lebanon a ranar Litinin, a cewar wata ƙungiyar da ke da alaƙa da ƙungiyar Amal mai ƙawance da Hizbullah.
An shafe makonni ana gwabza fada a kan iyakar Lebanon da Isra’ila, inda ake samun karuwar asarar rayuka daga bangarorin biyu da kuma yaƙin bakan da ke ƙara rura wutar rikicin da ke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta Lebanon da ke samun goyon bayan Iran.
Hezbollah dai na ci gaba da musayar wuta da sojojin Isra’ila tun bayan da ƙawarta Hamas ta Falasdinawan ta shiga yaƙi da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Harin na Isra’ila ya kashe mutum biyu a kudancin Lebanon a ranar Litinin, a cewar wata ƙungiyar da ke da alaƙa da ƙungiyar Amal mai ƙawance da Hizbullah.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya rawaito cewa, a ɓangaren Isra’ila, wani harin makami mai linzami da kungiyar Hizbullah ta kai a ranar Lahadin da ta gabata ya raunata ma’aikata da dama na Kamfanin Lantarki na Isra’ila kuma mutum ɗaya ya mutu sakamakon raunin da ya samu a ranar Litinin.
Musayarwar wutar ita ce tashin hankali mafi muni da aka gani a kan iyakar tun bayan da Isra’ila da Hizbullah suka gwabza yaƙi na tsawon wata guda a shekara ta 2006.
Ya zuwa yanzu, sama da ‘yan kungiyar Hizbullah 70 da fararen hula 10 aka kashe a kasar Lebanon, sannan an kashe mutane 10 da suka hada da sojoji bakwai a Isra’ila. Wasu dubbai daga bangarorin biyu sun tsere daga hare-haren harsasai.
Ƙaruwar hare-hare
Shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya fada a ranar Asabar din da ta wuce cewa fagen daga na Lebanon zai ci gaba da “zama wani wajen ci gaba da aiki”, yana mai cewa “ana samun ci gaba mai yawa” kan saurin ayyukan kungiyar.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gargadi Hezbollah a ranar Litinin da kada ta fadada hare-harenta
“Wannan wasa da wuta ne. Za mu ba da amsar wuta da wuta mafi ƙarfi. Ka da su zungure mu, domin abin da muka yi zuwa yanzu kaɗanmuka nuna daga cikin ƙarfinmu,” in ji shi a wata sanarwa.
Da aka tambaye shi a wani taron manema labarai a ranar Asabar kan ko me Isra’ila ke nufi da jan layi, sai Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce: “Idan kuka ji cewa mun kai hari Beirut, za ku fahimci cewa Nasrallah ta ƙetare wannan layin.
Ramuwa
Firayi ministan riƙon ƙwarya na kasar Labanon Najib Mikati, a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera a jiya Lahadi, ya ce ya sake samun ƙwarin gwiwa da “ayyukan” Hizbullah ya zuwa yanzu.
Muna kiyaye kamun kai, kuma ya rage ga Isra’ila ta daina tsokanar da take ci gaba da yi a kudancin Lebanon,” in ji shi.
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayyana tashin hankalin a matsayin “zungure ni in zungure ka tsakanin kungiyar Hizbullah ta Lebanon da sojojin Isra’ila a arewacin kasar”, yana mai hasashen Isra’ila za ta ci gaba da mai da hankali kan barazanar Hizbullah.
“Kuma tabbas babu wanda ke son ganin wani rikici ya sake ɓarkewa a arewacin kasar kan iyakar Isra’ila da gaske,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai a birnin Seoul, ko da yake ya ce da wuya a iya hasashen abin da ka iya faruwa.