Harin Isra’ila kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia a Gaza ya kashe sama da mutum 30 – Hamas
Harin Isra’ila kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia a Gaza ya kashe sama da mutum 30 – Hamas
Isra’ila ta kwashe kwana 38 tana luguden wuta a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 11,100, ciki har da mata da kananan yara fiye da 8,000, tun bayan da Hamas ta kai mata harin ba-zata ranar 7 ga watan Oktoba.
Gaza
1909 GMT — Sama da mutum 30 sun mutu sakamakon harin da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia a Gaza – Hamas
Fiye da mutane 30 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin bam da Isra’ila ta kai a sansanin ‘ayn gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza, in ji kafar yada labaran Hamas.
1336 GMT — Rashin man fetur zai dakatar da ayyukan agaji a Gaza nan da awa 48 — MDD
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu UNRWA ta yi gargadin cewa ayyukanta a Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita za su dakata nan da kwana biyu saboda ƙarancin man fetur yayin da ake gwabza fada tsakanin Isra’ila da Hamas.
Aikin jinƙai a Gaza zai tsaya cak a cikin sa’o’i 48 masu zuwa saboda ba a bar wani man fetur ya shiga Gaza ba,” kamar yadda shugaban UNRWA na Gaza Thomas White ya rubuta a shafinsa na X.
1221 GMT — Isra’ila ta yi asarar ayyuka 950,000 a rikicin Gaza
An kiyasta cewa fannin tattalin arzikin Isra’ila ya yi asarar ayyuka kusan 950,000 tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza a watan jiya, a cewar alkaluman hukuma.
Adadin marasa aikin yi a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 3.2 a cikin watan Satumba daga kaso 3.1 cikin 100 a cikin watan Agusta, kamar yadda hukumar Kididdiga ta Tsakiya (CBS) ta nuna.
An kiyasta adadin ma’aikata a Isra’ila sun kai kusan miliyan hudu, a cewar CBS.
Sakamakon barkewar rikicin Gaza, sama da ma’aikatan Falasdinawa 178,000 ne suka kasa tsallakawa cikin Isra’ila, a cewar Hukumar Kididdiga ta Falasdinu.
1000 GMT — Jiragen ruwan Turkiyya ɗauke da kayayyakin asibitocin tafi da gidanka sun isa Masar ta kusa da Gaza: Jami’ai
Wani jirgin ruwan Turkiyya ɗauke da kayayyakin kafa asibitocin wucin-gadi sun isa tashar jiragen ruwa ta El Arish a Masar a kusa da kan iyakar Rafah da Gaza, a cewar wani jami’in tashar jiragen ruwa.
Wani ma’aikacin lafiya na Turkiyya ya ce jirgin na ɗauke ne da “injinan janareto da motocin asibiti don kafa asibitoci takwas.
Kayan sun isa ne a yayin da dukkan asibitocin Gaza “suka daina aiki” sakamakon yaƙin da dakarun Isra’ila ke ci gaba da yi, a cewar jami’an yankin.
0922 GMT — Isra’ila ta sake kai hari hukumar MDD ta ƴan gudun hijira a kudancin Gaza
Hukumar Bayar da Agaji ga Falasɗinawa Ƴan gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce rundunar sojin sama ta Isra’ila kai hari kan ɗaya daga cikin cibiyoyinta a kudancin Gaza, duk da cewa an samu ƙwarya-ƙwayar hadin gwiwa tare da bangarorin da ke fada junan.
UNRWA, ta ce harin wanda aka kai a ranar Lahadi ya haifar da “mummunar ɓarna” a masaukin baƙinta da ke Rafah, in da ta ƙara da cewa ba a samu asarar rai ba tun lokacin da ma’aikatan MDD suka bar wurin mintuna 90 kafin harin.
Wannan harin na baya-bayan nan dai wani lamari ne da ke nuni da cewa babu wani wuri a Gaza da ke da tsaro.
“Ba arewa ba, ba tsakiya ba kuma ba kudu ba,” in ji kwamishinan UNRWA – Janar Philippe Lazzarini.
0727 GMT — Yawan wadanda suka mutu a asibitin Al Shifa ya karu yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza
Wani darakta na asibitin Al Shifa ya ce adadin wadanda suka mutu ya haura 20, ciki har da jarirai shida.
Wani jariri da bai kai lokacin haihuwa ba da wasu majinyata biyu sun mutu a asibitin Al Shifa na Gaza, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Gaza na Falasdinu, yayin da wurin ya fuskanci ƙarancin man fetur a yayin da Isra’ila ke kai hare-hare a yankin da ke kewaye.
Youssef Abu Rish, mataimakin ministan lafiya a Gaza ya ce sabbin wadanda suka mutu sun kai adadin zuwa jarirai bakwaini guda da kuma marasa lafiya tara, tun bayan da ƙarancin wutar lantarki ya fara shafar asibitin a kwanakin da suka gabata.
Wani darakta na asibitin Al Shifa ya ce adadin wadanda suka mutu ya haura 20, ciki har da jarirai shida.
0809 GMT — Falasɗinawa na barin asibiti mafi girma a Gaza: MDD
Falasɗinawa da dama da suka rasa muhalkansu tare da marasa lafiya da aywa sun bar asibiti mafi girma a Gaza, wanda ke zagaye da dakarun Isra’ila, a cewar wani jami’in lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Kimanin marasa lafiya 650 da ma’aikatan kiwon lafiya 500 da kuma mutum 2,500 da aka yi ƙiyasin cewa sun rasa matsugunansu, sun kasance a harabar asibitin Shifa, in ji Mohammed Zaqout, daraktan asibitoci a Gaza.
Wannan na nuna alamar gagarumin tashin mutane tun ƙarshen mako lokacin da jami’an kiwon lafiya na Gaza suka ce kusan marasa lafiya 1,500, tare da ma’aikatan lafiya 1,500 da kuma mutum 15,000 da suka rasa matsugunansu suna Shifa.
Al’amura dai sun taɓarɓare a garin Shifa a ƙarshen makon da ya gabata, inda likitoci suka bayyana cewa mai ya ƙara a janareto na ƙarshe da ya rage yana aiki, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka haɗa da jarirai bakwaini.
Jami’in na MDD ya ce da yawa daga cikin mutanen da suka rasa matsugunan sun tsere daga harabar, kuma wasu iyalai sun dauki ‘yan’uwansu da raunukansu ba su ta’azzara ba, sun tafi da su.
0421 GMT — Majalisar Dinkin Duniya na alhinin rasuwar ma’aikatanta a Gaza
An yi kasa-kasa da tutocin Majalisar Dinkin Duniya a ofisoshinta da ke fadin nahiyar Asiya, sannan ma’aikata sun yi tsit na minti daya domin tunawa da abokan aikinsu da Isra’ila ta kashe sakamakon luguden wuta a Gaza.
An yi kasa-kasa da tutocin masu launin shudi da fari da misalin karfe 9:30 na safe a agogon biranen Bangkok, Tokyo da Beijing, kwana guda bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahotanni na “mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu” a hare-haren da Isra’ila ta kai a ofisoshinta da ke Gaza.
Hukumar Bayar da Agaji ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ranar Juma’a ta ce an kashe ma’aikatanta fiye da 100 tun lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza.
Source: TRTHausa