Isra’ila ta sake kashe Falasdinawa shida a hare-haren da take kaiwa cikin dare a Gabar Yamma da Kogin Jirdan da Isra’ilar ta mamaye, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta bayyana a ranar Talata.
Falasdinawa biyar aka kashe a birnin Tulkarem a wani harin sama da Isra’ila ta kai wanda kuma ya raunata mutum tara, inda mutm uku ke cikin hali mai tsanani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya tabbatar.
Haka kuma akwai karin Bafalasdine guda da Isra’ila ta kashe a kusa da birnin Hebron, inda Isra’ilar ta yi ikirarin ya yi niyyar kai musu hari da wuka.
#BREAKING: Another #Palestinian shot dead by Israeli forces in Tulkarm. pic.twitter.com/NDm7Z4xNgV
— Wafa News Agency – English (@WAFANewsEnglish) November 13, 2023
0750 GMT — Lauyoyin Falasdinawa sun shigar da Isra’ila kara a Kotun ICC
Lauyoyin wadanda hare-haren Isra’ila suka fadamawa a Gaza sun shigar da kara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC da ke birnin Hague na Netherlands.
Wakilin jama’ar Gaza a kotun ICC wato Gilles Devers da wasu mutum hudu da suka masa rakiya domin kai korafin sun bayyana cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a kan Gaza wadanda suka hada da kisan kare-dangi.
Isra’ila ta kashe sama da mutum 11,180 a Gaza wadanda akasarinsu yara ne tun daga 7 ga watan Oktoba.
Falasdinawa biyar aka kashe a birnin Tulkarem a wani harin sama da Isra’ila ta kai wanda kuma ya raunata mutum tara, inda mutm uku ke cikin hali mai tsanani, Falasdinawa biyar aka kashe a birnin Tulkarem a wani harin sama da Isra’ila ta kai wanda kuma ya raunata mutum tara, inda mutm uku ke cikin hali mai tsanani.
Source: TRTHAUSA