Yayin da ‘yan Nijeriya suka bi sahun daukacin ‘yan uwa Musulmi don gudanar da shagulgulan bukukuwan babbar Sallah, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa yana aiki ba dare ba rana don lalubo mafita kan kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.
Tinubu, a cikin sanarwar da ya rattaba wa hannu a ranar Talata, ya sanar da cewa, matakan da gwamnatinsa ta dauka, za ta mayar da hankali wajen sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya da kuma magance daukacin abubuwan da ke hana kasar ci gaban kasa.
“A yanzu haka Nijeriya na ci gaba da fuskantar kalubale, musamman na tattalin arziki da kuma kalubalen rashin tsaro.
“Muna sane da wadannan kalubalen, ina kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, kalubalen za a shawo kansu.”
Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu kwarin guiwa don a samar da gobe mai dorewa duk da kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.
Ya kuma taya ‘yan kasar murnar babbar Sallah, inda ya yi kira ga ‘yan uwa Musulmi da su yi amfani da Sallar wajen taimaka wa marasa karfi.
Ya ce, “dole ne mu godew a Allah SWA bisa damar ya ba mu ta ganin wannan ranar ta Sallah, inda ya yi nuni da cewa, hanyar da ya fi dacewa mu nuna farin ciki shi ne mu ci gaba da zama lafiya da kowa da nuna kishin kasarmu Nijeriya.
A cewarsa, “dole mu ci gaba da yin koyi da halayen kakanmu Annabi Ibrahim ta hanyar yi wa Allah bauta da nuna hakuri da kuma son junanmu.”
Tinubu ya gudanar da Idi a Masallacin Idi da ke Obalende Eid daura da gidan barkin soji na Dodan.