Bincike ya nuna jirage sama da 30 suka sauka a babban filin jirgin Yakubu Gowon da ke garin Jos.
Jiragen sama na yawo da masu saukar ungulu sun yi ta shawagi yayin da APC ta fara yin kamfe.
Manyan ‘yan siyasa sun je Filato domin yi wa Bola Tinubu yakin neman zaben shugaban kasa.
Punch ta fitar da rahoto cewa duk manyan ‘yan jam’iyyar APC sun halarci kaddamar da yakin neman zaben Bola Tinubu a Jos a jihar Filato.
Jiragen sama fiye da 30 aka samu labarin sun sauka a filin tashin jirgi na Yakubu Gowon a ranar Talata da APC ta soma yakin zaben shugaban kasa.
Jirage sama mai daukar daidaikun mutane da masu saukar ungulu da na yawo da na manyan kamfanoni sun yi ta shawagi a babban birnin na Filato.
Jirage sama mai daukar daidaikun mutane da masu saukar ungulu da na yawo da na manyan kamfanoni sun yi ta shawagi a babban birnin na Filato.
An ga jiragen sama irinsu Bombardier Challenger 601, Hawker Siddeley HS 125, Learjet 45, Challenger 601, United Aviation HS125, da Gyro Air HS125.
Rahoton yace an ga tashi da saukar jiragen Triaxell Gulfstream IV, Learjet 45, Beechcraft B190, Challenger 601, da kuma Dornier Aviation D328 a jiya.
Akwai jiragen yawo irinsu Embraer E145, Embraer 135, da Bombardier Challenger CRJ9 da suka sauka a garin, baya ga jirgin fadar shugaban Najeriya.
Sanata Shehu Sani ya soki yadda ake yawo da jirgin fadar shugaban kasa zuwa wajen taron siyasa.
‘Dan adawar siyasar yace yin hakan bai dace ba.
Manyan baki a Jos Kakakin PCC, Festus Keyamo a shafinsa na Twitter, ya tabbatar da duka gwamnonin APC sun je wajen kaddamar da takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima.
Wadanda aka gani a wajen taron yakin neman zaben sun hada da shugaban majalisa, Ahmed Lawal da ma sauran ‘yan majalisa daga wasu jihohin.
An ga Gwamnoni: Ben Ayade; Nasir El-Rufai; Mala Buni; Hope Uzodimma; Simon Lalong; Yahaya Bello; Abdullahi Sule da mataimakin gwamnan Legas.
Rahoton yace akwai tsofaffin gwamnoni kamar; Mohammed Abubakar, Dr. Kayode Fayemi, Ali Modu Sheriff, da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Ina aka samu kudin nan?
An ji labari Buba Galadima yace duk dukiyar da Bola Tinubu ko Atiku Abubakar suke takama da ita, kudin sata ne da ake shirin sayen kuri’u a zaben 2023.
Neman takarar shugaban kasa sai da kudi, Buba Galadima yace jam’iyyarsu ta NNPP ba ta da kudin da ya wuce mutanen da Dr. Rabiu Kwankwaso ya gina.
Source:LegitHausa